An yiwa Paparoma Francis kyakkyawar tarba a Uganda

Image caption Paparoma Francis ya sauka a Uganda

Fiye da matasa 'yan kasar Uganda dari da hamsin ne su ka yiwa Paparoma Francis kyakykyawar tarba a wajen birnin Kampala babban birnin kasar.

Paparoma Francis ya bukace su da suyi amfani da kaifin imaninsu wajen fuskantar duk wani kalubalen rayuwa.

A wajen gangamin tarbar Paparoman, ya gana da wata mata wacce a ka haifa da kwayar cutar AIDS mai karya garkuwar jiki da kuma wani mutum wanda 'yan tawayen LRA su ka yi garkuwa da shi.

Tunda farko, dubban mutane ne su ka halarci taron addu'o'i da Paparoman ya jagoranta.

A gobe ne Paparoma Francis zai isa kasa ta karshe a cikin jerin kasashen da zai ziyarta wato Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.