A na zaben shugaban kasa a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yau Lahadi ake zaben shugaban kasa a Burkina Faso

A yau ne al'ummomin kasar Burkina Faso za su fita kada kuri'a domin zaban sabon shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki.

Wannan shi ne zabe na farko a kasar tun bayan boren da jama'ar kasar suka yi bara, wanda ya raba shugaban kasar da yafi dadewa Blaise Compaore da mulkin kasar.

A cikin watan daya gabata ne a ka so a gudanar da zaben, amma hakan bai yiwuba saboda yunkurin juyin mulki da wasu sojoji a kasar suka yi da ba su samu nasara ba.

Zaben zai kawo karshen gwamnatin rikon kwarya da aka kafa a kasar bayan hambarar da Mista Compaore, kuma masu aiko da rahotanni sun ce, wannan zai iya zama zabe irin sa na farko a tarihin kasar da a ka bai wa jama'a damar shiga.