Kun san illar sauyin yanayi?

Hakkin mallakar hoto PA

Shugabannin kasashen duniya kusan 150 na hallara a Paris cikin tsatsauran matakan tsaro domin babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi.

Za a fara taron -- wanda aka yi wa lakabi da COP21 -- ranar Litinin, zai kuma yi kokarin samar da yarjejeniya ta dogon-zango kan yadda za a rage fitar da gurbataccen hayaki a duniya.

Sai dai kasashen duniya matalauta sun ce suna fargabar za a "bar su a baya" a yayin da ake kokarin cimma matsaya kan sabuwar dokar da za a samar kan sauyin yanayi.

Masu sharhi sun yi ce harin ta'addanci na baya bayan nan da aka kai a babban birnin Faransa zai karfafa yiwuwar cimma sabuwar yarjejeniyar kan sauyin yanayi.

Mutane kimanin 40,000 ne ake sa ran za su halarci taron wanda zai ci gaba har zuwa ranar 11 ga watan Disamba.

Halarta taron sun hada da shugabannin kasashe da gwamnatoci 147.