Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mutane 18 sun mutu a Syria

Image caption Tun shekarra 2011 ake rikici a Syria.

Wani jirgi Yaki maras matuki da ake kyautata zaton na na Rasha ne ya hallaka akalla mutane 18 tare da jikkata wasu da dama a garin Ariha da ke yankin Idlib a rewacin kasar Syria.

Kafar yada labaran 'yan adawa da kungiyar da kare hakkin bil'adama a Syria sun rawaito cewa lamarin ya faru ne a wata kasuwa, haka kuma harin ya ruguje wasu manyan gine-gine guda uku da ke garin.

Ga rahoton da Badriyya Tijjani Kalarawi ta hada mana.