Ana tsangwamar Musulmai a Australia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Musulmai sun ce suna zaune lafiya da wadanda ba Musulmai ba.

Wani bincike da aka yi a Australia ya nuna cewa Musulmai na fuskantar tsangwama sau uku fiye da wadanda ba Musulmai ba.

Kusan kashi 60 cikin dari na Musulman da aka yi wa tambayoyi sun bayyana cewa ana nuna musu wariya da musgunawa a kasar.

Mahalarta wani taro da aka yi kan Musulinci a birnin Sydney, sun yi gargadin cewa nunawa Musulmai wariya da kyama zai sa matasansu su iya fadawa cikin kungiyoyin da ke da tsattsauran ra'ayin addini.

Sai dai sama da kashi 85 cikin dari na mutanen sun bayyana cewa dangantaka tsaknin Musulman kasar da wadanda ba Musulmai ba tana da kyawu.