Kamfanin sigari na bada cin hanci a Afrika

Image caption Miliyoyin 'yan Afrika na shan sigari

BBC ta bankado shaidun cin hanci da rashawa a kamfanin yin tabar sigari na British American Tobacco a Afirka.

Binciken da aka gudanar, ya gano cewa kamfanin ya bai wa 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnatoci a kasashen yankin gabashin Afirka cin hanci.

An ba da kudadan da ba bisa ka'ida ba, domin kashewa sauran kamfanoni tabar sigari kasuwa da kuma raunana dokar yaki da shan tabar sigari.

Wani mai kwarmata bayanai ne, ya fallasa lamarin inda ya bayar da daruruwan takaddun da suke kunshe da bayanai.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kamfanin tabar sigarin na Britsih American Tobacco ya ce dama masu zargin na sa na da wata kullalliya da shi, kuma sam shi bai yadda da cin hanci ba.