Mutanen gari sun kashe firsunoni 4 a Guinea

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan sanda a Guinea

Rahotanni daga kasar Guinea sun ce wasu mutane sun cusa kai cikin wani gidan yari, inda suka kashe fursinoni hudu da ake tsare da su, wadanda ake zargi da kisan kai.

Ganau da kuma wasu jami'an gidan yarin sun ce jita-jitar da aka rika yadawa a garin Kouroussa cewa ana shirin sakin mutanen hudu ita ce ta janyo mutanen garin da suka fusata dannawa gidan yarin.

Ana zargin fursinonin ne da kashe wani dillalin gwal a farkon wannan watan.

Uku daga cikinsu, dukan tsiya ne ya kashe su, yayin da cikon na hudun kuma aka kona shi da ransa.