Nijar: Alkalai sun gargadi Bazoum

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bazoum ne shugaban jam'iyyar PNDS mai mulki

Kungiyar alkalai a Jamhuriyar Nijar, ta nuna rashin jin dadinta ga wasu kalamai da ta ce za su iya haddasa fitina, da ta ce minista Mohamed Bazoum na jam'iyyar PNDS ya yi.

Kungiyar ta ce ba za ta taba yarda ba, 'yan siyasa su rika tozartar da su domin abin da ta kira biyan bukatun kansu.

Kungiyar alkalan da ake kira 'Saman' ta yi kira ga alkalai masu gabatar da kara su tuhumi minista Bazoum game da kalaman da ya yi.

Shi dai Mista Bazoum ya yi zargin cewa madugun 'yan adawa, Hama Amadou ya bai wa wasu alkalai toshiyar baki a kan shari'arsa da ake yi, zargin da suka musanta.

Sai dai alkali mai gabatar da kara a babbar kotun Yamai, mai shari'a Shu'aibu Sumana ya ce ba zai ce uffan ba dangane da lamarin.