Blackberry zai fice daga Pakistan

Hakkin mallakar hoto Blackberry
Image caption Wayar Blackberry Passport

Kamfanin wayoyin Blackberry ya ce zai dai na hulda a kasar Pakistan a karshen shekaran nan ta 2015, saboda bukatar da gwamnatin kasar ta gabatar masa na sa ido a kan bayanan masu amfani da wayoyin.

Gwamnatin Pakistan ta ce tana so ta samu damar sa ido a kan dukkan sakonni da email da mutane suke aikawa da wayoyin Blackberry.

A shafin sa na intanet, kamfanin wayoyin Blackberry ya ce ya yanke shawarar ya fice daga kasar ne saboda wannan takaddama.

Kamfanin ya ce gwamnatin Pakistan din ba ta yi bukatar ba ce don tabbatar da tsaron jama'a, ta yi hakan ne domin ta samu damar shiga runbum bayanan kamfanin.

Tun a watan Yuli hukumar da ke kula da sadarwa ta Pakistan ta shaida wa kamfanin Blackberry cewa ba za a bar shi ya ci gaba da gudanar da tsarin aikawa da sakonni ba a kasar saboda dalilai na tsaro.

Jami'in kamfanin Marty Beard ya ce gaskiyar magana ita ce gwamnatin Pakistan din tana so ne ta rika ganin dukkan bayanan da zasu rinka bi ta wayoyin Blackberry, kuma kamfanin ba zai yadda da hakan ba.

Mista Beard ya ce ci gaba da hulda a Pakistan, yana nufin kamfanin ya karya dokokinsa na sirranta bayanan mutane.

Ya ce wannan ba abu ne da kamfanin zai lamunta ba.