Yaudara ce ta haddasa Boko Haram— Kukah

Hakkin mallakar hoto kukahfacebook
Image caption Bishop Mathew Hassan Kukah

A Najeriya wani fitaccen limamin darikar Roman Katolika ya ce shugabannin yankin arewacin kasar mai fama da rikicin Boko Haram, su ne ummulhaba'isun bullar kungiyoyi irin su Boko Haram.

Bishop Mathew Hassan Kukah ya ce kokarin kafa daular musulunci da 'yan kungiyar ke yi, ya samo asali ne daga alkawurran da shugabannin yankin suka yi wa talakawa na kafa shari'ar musulunci a yankin, alhali ba da gaske suke yi ba.

Bishop Kukah ya yi wadannan kalaman ne cikin wata kasida da ya gabatar a wajen wani taro da wata cibiyar kula da jin dadin al'ummar musulmi ta shirya a wata jami'a da ke birnin Oshogbo.

Ya ce in ana maganar musabbabin Boko Haram, ba ana nufin bullar Muhammad Yusuf da mabiyansa ba ne, domin akwai abubuwa masu nasaba da kungiyar da suka faru kafin a san Muhammad Yusuf.

Ya ce take-taken 'yan siyasar arewa game da addinin musulunci tun kimanin shekaru 20 da suka wuce, idan an je wurin taron gyara kundin mulkin kasa, sai su yi ta babatun cewa su sharia su ke so.

Bishop Kukah ya ce amma kuma 'yan siyasar ba da gaske su ke yi ba game da maganar kafa shari'ar musulunci a yankin.