'Yan bindiga sun kai wa Jonathan hari

Image caption Tshohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Rahotanni daga kudancin Najeriya sun ce tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka danna cikin ayarin motocinsa a Yenagoa.

Rahotannin suka ce 'yan bindigan sun ratattaki motocin da tsohon shugaban ke tafiya a cikinsu ne har zuwa gidansa dake Yenagoa.

Daga baya, jami'an tsaro dake kare Dr. Jonathan din sun fi karfin 'yan bindigan, inda suka kama su.

Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar wa 'yan jarida cewa ana gudanar da bincike kan 'yan bindigar da aka kama.

Sai dai, wasu rahotannin sun tsinkayi rundunar 'yan sandan ta na cewa, mai yiwuwa 'yan bindigan sun danna cikin jerin motocin tsohon shugaban ne bisa kuskure.