Boko Haram: An kai hari a Diffa

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a Jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar.

A jamhuriyar Nijar, mazauna kauyen Gamgara da ke Jihar Diffa sun shaida wa BBC cewa wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane 6 a wani hari da suka kai kauyen.

Rahotanni sun ce an kone yawancin gidaje, kuma ana zargin sun gurbata ruwan rijiyar kauyen da guba, saboda kumfar da ya ke ta yi.

Kawo yanzu hukumomin kasar ba su ce komai ba dangane da harin

'Yan kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a Jihar Diffa, inda suka kashe mutane da dama.