Tattalin arzikin Brazil na samun koma baya

Hakkin mallakar hoto ABr
Image caption Tattalin arzikin Brazil na samun koma baya

Wadansu sabbin alkaluma sun nuna cewar koma bayan tattalin arzikin kasar Brazil ya tsananta.

Tattalin arzikin kasar wanda shi ne mafi girma a kudancin Amurka, ya ragu da kusan digo biyu cikin dari a watanni ukun karshen shekara, hakan kuma mafi muni ga kasar a kusan shekaru ashirin.

Zuba jari, da yawan kayayyakin da kasar ta ke samarwa da kuma yadda kasar ta ke amfana da kayayyakin sun yi kasa sosai.

Kikikaka da aka samu a majalisar dokokin kasar ta kuma sa sauye-sauyen tattalin arziki sun tsaya cak, sannan ga wata babbar badakala da ta danganci almundahana a kamfanin mai na kasar wato Petrobas.

Matsalolin tattalin arziki na dakile kudaden harajin da gwamnatin kasar ke samu, sun sanya ba a gudanar da ayyukan da ya kamata a gudanar a kasar.