An sake kama Sambo Dasuki

Sambo Dasuki

Hukumar tsaro ta farin kaya a Nigeria DSS ta kame tsohon mai bawa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

Wata cibiyar da ke watsa bayanai da ke da kusanci da Sambo Dasukin mai suna PR Nigeria ce ta bayyana haka a wani sako da ta aike wa manema labarai.

Babu dai wata sanarwa da ta fito daga hukumar ta DSS game da kame Sambo Dasuki.

Hukumomin Nigeria suna tuhumar Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ne da yin sama da fadi da kudaden da suka kai dalar Amurka biliyan biyu ta sayen makamai.

Wani kwamiti da gwamnatin Nigeriar ta kafa ne ya ce ya bankado almundahanar.

Shi dai Sambo Dasuki ya ce babu wanda ya tuntube shi game da zargin ya kuma musanta yin sama da fadi da kudaden gwamnati.

Ita mai dai hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC a Nigeriar ta kama tsohon minista a ma'aikatar kudi ta kasar Bashir Yuguda bisa zargin yana da hannu a badakalar kudaden na dala biliyan biyu.