Kai tsaye: Mata 100, rabin al'ummar duniya

Latsa nan domin sabunta shafin:

Image caption Mata na fuskantar tsangwama daga wajen al'uma. Shin yaya za a kawo karshen wannan matsala?

A ci gaba da shirinmu na "mata 100, rabin al'umar duniya", yau za mu kawo muku muhawara kai tsaye kan kalubalen da mata ke fuskanta.

Mun kammala kawo muku bayanai kai-tsaye game da "Mata 100, Rabin Muryar Al'umar Duniya". Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu. Mun gode

Image caption Halima Umar Saleh ce ke jagorantar shirin.

3:19 Ka da ku manta, muna gabatar muku da bayanai ne kai-tsaye game da muhawara kan "Mata 100, Rabin Muryar Al'umar Duniya".

Image caption Faleela Mohammed ta yadda cewa dole ne ma'aurata su rika taimakawa juna domin zama zai fi yin dadi.
Image caption A daina barin mata suna yin shugabanci, in ji Ziya'atulhaq

2:47 Ziya'atulhaq Usman ta ce bai kamata a rika barin mata suna shugabanci ba saboda, a ganinta, tunda Alkur'ani bai amince su yi shugabanci ba, ya kamata su guji nemansa.

Image caption Ayisha Osore ta dade tana fafutikar ganin mata sun samu 'yanci a Najeriya.

2:23 Mata na ci gaba da yin tsokaci kan kalubalen da suke fuskanta da hanyoyin da za su shawo kansu.

Image caption Amina Bello Rundawa ta ce akwai bukatar bai wa mata ilimi domin hakan zai taimaka musu wajen samun mafita a rayuwa.

12:58 Hauwa Mohammed ta ce ya kamata mata su rika yi wa maza biyayya, amma bai kamata maza su hana mata neman na-kai ba.

12:35 Bara'atu Aliyu ta ce ba sai mace tana da kyau ba za ta taka rawa wajen ci gaban dan adam. Ta bayar da misalan mata da dama da ta ce ba kyawawa ba ne, amma suna yin zarra a fannonin rayuwa daban-daban.

Image caption 100 women yana cikin maudu'an da suka fi jan hankalin masu amfani da Twitter a Nigeria
Image caption Mata 'yan jarida a Najeriya na bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban al'umma.

11:56 Mun kammala zagayen farko na muhawarar da muke yi kan kalubalen da mata ke fuskanta.

Image caption Rafat Salami ta ce maza da dama a wurin aikinta suna mayar da ita kamar boyi boyinsu.

11:28 Shin ya kamata mata su zama boyi boyin maza?

Image caption Hajiya Sani, mataimakiyar darakta a gidan rediyon Voice of Nigeria, ta ce ta yarda cewa kyawu yana taka rawa ga mata a wuraren ayyukansu domin samun daukaka, amma dole sai hakan za hadu da kwazon mace. Menene ra'ayinku?

11:15 Lydia Samson ta ce ba sai mace tana da kyau ba za ta iya yin zarra a wurin aikinta.

10:55 Rafat Salami ta gidan rediyon Voice of Nigeria ta ce akwai gagarumar rawar da mata za su taka wajen inganta rayuwar al'umma.

Image caption Rahama Sa'id ta ce addini da al'adun mace ne za su taka rawa wajen bunkasar rayuwarta.

10:20 Wasu alkaluma sun nuna cewa maza sun fi mata yawa a harkokin watsa labarai. Ta yaya za a cike wannan gibi?

Image caption Lydia Samson na cikin fitattun mata 'yan jarida a gidan talabijin na Najeriya, NTA. Tana taka muhimmiyar rawa wajen ganin mata sun yi zarra a fannonin rayuwa daban-daban.

09:43 Za mu gudanar da muhawarar ce da rukunai hudu na mata, kuma za mu fara da mata 'yan jarida.