Kawunan 'yan majalisar Biritaniya sun rabu kan IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cameron ya ce 'yan kungiyar IS dabbobi ne.

An samu rabuwar kawuna a tsakanin 'yan majalisar dokokin Biritaniya kan yunkurin da kasar ke yi na shiga kawancen sojin da Amurka ke jagoranta a yaki da kungiyar IS.

Firai Ministan kasar, David Cameron, ya ce IS na yin barazana ga tsaron Biritaniya, yana mai cewa mayakansu na yi wa mata fyade da kashe Musulmai, "kuma dabbobi ne".

Sai dai shugaban jam'iyyar hamayya, Jeremy Corbyn, yana adawa da shigar Biritaniya cikin kawancen, yana mai cewa sojin kasar za su rika kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

A cewarsa, miliyoyin 'yan Syria na son a sasanta domin kawo karshen yakin basasar kasar.