Biritaniya za ta aika karin jirage Syria

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Jiragen Biritaniya sun kai hari kan yankuna shida da ke karkashin ikon IS.

Sakataren tsaron Biritaniya, Michael Fallon, ya ce kasarsa za ta aike da karin jiragen sama domin su taimakawa dakarun kasar da ke yin ruwan bama-bamai kan 'yan kungiyar IS a Syria.

Mista Fallon ya ce Biritaniya za ta ninka adadin jiragen da ta yankin gabas ta tsakiya, sa'o'i kadan bayan jiragenta sun kai harin farko a kan mayakan IS.

Jiragen dai sun yi luguden wuta ne a yankin Omar da ke da rijiyoyion mai a gabashin Syria.

Ya kara da cewa za su hana IS ci gaba da hakar man fetur domin su daina samun kudin da suke amfani da shi wajen shirya hare-hare.

A ranar Laraba ne majalisar dokokin Biritaniya ta amince da kudurin dokar da ya bai wa kasar izinin kai hare-haren kan mayakan IS.