Ta'addanci: Dan Biritaniya zai sha dauri a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jermaine Grant ya musanta aikata laifukan.

Wata kotu a kasar Kenya ta yanke wa wani dan Biritaniya hukuncin shekaru tara a gidan yari bayan ta same shi da laifukan ta'addanci.

A farkon wannan shekarar dai, wata kotu a Mombasa ta wanke Jermaine Grant daga laifukan, sai dai kotun tarayya ta Kenya ta soke hukuncin.

Kazalika yana fuskantar zargin laifukan "hada abubuwan da ke fashewa", kuma ana ci gaba da yi masa shari'a kan batun.

Mista Grant ya musanta aikata laifukan.