Rikici ya barke a Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikici ya barke a Bujumbura babban birnin kasar Burundi

Rahotanni sun ce an kashe mutane akalla tara a daren jiya a Bujumbura babban birnin kasar Burundi.

Wadanda suka rasa rayukan nasu sun hada da fararen hula takwas da dan sanda guda.

An dai ji karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa a wurare daban-daban da ke birnin.

An kashe mutane fiye da 200 tun daga watan Afrilu bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da batun tsayarwarsa takara a karo na uku.

Wani jagoran masu fafutuka a wata kungiyar kare hakkin dan-adam a Burundi ya shaida wa BBC cewa, takunkumin da aka sanyawa wasu jami'an gwamnati hudu da kuma tsoffin jami'an gwamnatin zai tursasawa mahukuntan kasar fara batun sasantawa.