An kashe mutane 14 a harbe-harbe a Amurka

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda a California

'Yan sanda a California sun ce sun kashe wani mutun da suke zargi yana daga cikin wadanda suka bude wuta a San Bernardino.

Mutane 14 ne aka kashe, sannan wasu 17 suka samu rauni a harin wanda aka kai a wani wurin bidiri.

'Yan sandan suna binciken wata mota da suke tunanin 'yan bindigar da suka kaddamar da harin sun yi amfani da ita lokacin da suka yi kokarin arcewa.

Kazalika 'yan sandan sun yi wa wani gida kawanya a yankin, inda suke sa ran wani daga cikin maharan yana boye.

Shugaba Obama ya yi kakkausar suka game da harin, inda ya ce kasar tana fuskantar irin wannan matsala ta kai wa tarin mutane hari da bindiga fiye da kowace kasa a duniya.

Harin na Laraba shi ne mafi muni tun bayan bude wutar da wani ya yi a wata makarantar firamare a 2012 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26.