An mika Dasuki ga EFCC

Image caption Ana tuhumar Sambo DAsuki da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta mika tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkar tsaro, Sambo Dasuki ga hedikwatar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Jami'an hukumar DSS ne suka kame Dasuki a ranar Talata, bayan sun yoi masa daurin talala a gidansa na tsawon wata guda.

A ranar Alhamis ne kuma babbar kotun tarayya da ke Abuja za ta yi zaman sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar inda take neman a soke belin da aka bai wa Dasukin.

A zaman karshe da aka yi na sauraron karar ne lauyan gwamnatin tarayya Mista Mohammed Diri, ya shaida wa kotun cewa sun shigar da bukata a gaban kotun daukaka kara, suna kalubalantar hukuncin babbar kotun na bayar da belin Sambo Dasuki.

Shi dai Dasuki ya musanta laifukan da a da ake tuhumarsa dasu na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma sama da fadi da dukiyar gwamnati kotun ta kuma bashi izinin fita kasar waje domin ya je a duba lafiyarsa.