An rataye wasu 'yan ta'adda a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 140 ne suka mutu a harin da aka kai a Peshawar.

Hukumomi a Pakistan sun ce sun rataye wasu masu ikirarin kishin Musulinci hudu saboda rawar da suka taka a harin da aka kai wata makarantar soji soji a Peshwarar.

Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 140, yawancinsu kananan yara.

Bayan an kai harin ne gwamnati ta kafa wata kotun soji da za ta yi hukunci kan hare-haren 'yan ta'adda.

Babban hafsan sojin kasar ya sanya hannu kan takardar kisan mutane kwanaki biyu da suka wuce, kuma wannan shi ne karon farko da aka yi hakan tun lokacin da Kotun Kolin kasar ta amince kotunan soji su rika yin aiki.