Assad ya yaba wa Rasha kan yaki a Syria

Image caption Shugabannin Russia da Syria suke gaisawa

Shugaban Syria Bashir al-assad ya ce shigar Rasha cikin yakin da ake yi a kasarsa da kungiyar IS ya sauya al'amura.

A wata hira da ya yi da gidan talbijin na kasar Cezkolovakia, Mista Assad ya ce shekara dayan da kasashen yammacin duniya suka yi suna luguden wuta a Syria ba ta hana mayakan kungiyar IS ci gaba da kai hare-hare ba.

Amma ya ce tun da Rasha ta shiga yakin, kungiyar ta IS da ma sauran masu ikirarin yin Jihadi suke raguwa.

Da aka tambaye shi kan harbo jirgin Rashar da Turkiyya ta yi a makon jiya, Mista Assad ya ce shugaban Turkiyya Recep Erdoan ya shiga cikin dimuwa ne kawai.