Shugaban Rwanda ya gargadi Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Kagame ya ce hawainiyar AMurka ta kiyayi ramar kasarsa.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya gargadi Amurka da kada ta tsoma baki cikin siyasar kasarsa, yayin da ake samun sa-toka-sa-katsi kan shirinsa na yin tazarce.

A shafinsa na Twitter Shugaba Kagame ya ce, 'yan Rwanda ne kawai suke da hurumin zabar wa kansu duk wani al'amari da ya shafi siyasa.

A ranar Talata ne jakadar Majalisar Dinkin Duniya ta Amurka, Samantha Power, ta ce dole shugaba Kagame ya sauka daga mulki a karshen wa'adinsa da zai cika a shekarar 2017, domin ya bai wa matasa masu tasowa damar zama shugabanni.

Tun bayan kisan kare-dangi da aka yi a shekarar 1994 a Rwanda, Mista Kagame yake kan karagar mulki.

A watan da ya gabata ne majalisar dokoki da ke Kigali babban birnin kasar, ta gabatar da wani kuduri da zai yi wa kundin tsrain mulkin kasar kwaskwarima domin abshi damar yin tazarce.