Al'amura sun lafa a Anambra

Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Shugaban IPOB, masu fafutukar ganin an kafa jamhuriyar Biafra.

A Najeriya, rahotanni daga garin Anaca da ke jihar Anambra sun ce yanzu kura ta lafa.

Hakan ya biyo bayan matakan da hukumomi suka dauka na shawo kan fitinar da ta kunno kai, da kuma shawarar da matasan Ibo masu neman kafa jamhuriyyar Biyafara karkashin kungiyoyin IPOB da MASSOB suka yanke na dage zanga-zanga da suke yi.

Tuni dai shugaban 'yan sanda a Najeriya ya bayar da umarnin tura karin 'yan sanda zuwa yankin na kudu maso gabas domin shawo kan masu zanga-zangar.

Wasu 'yan kabilar Igbo da ke zaune a arewacin kasar sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da zanga-zangar da masu neman kafa kasar Biafra ke yi.