Ba sauran masu Ebola a Liberiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu masu aikin lafiya lokacin matsanancin fama da cutar ta Ebola a Liberiya.

A kasar Liberiya, mutane biyu na karshe da ke fama da cutar Ebola sun warke.

Mutanen sun kamu da cutar ne, a barkewar da ta sake yi a kasar.

Kasashen Liberiya da Guinea da Sierra Leone sun shafe shekaru biyu suna fama da cutar ta Ebola, inda ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Cutar ta sanya mata da yara da dama cikin halin maraici da takaba a kasashen.

A watan Yulin bana ne dai hukumar kula da lafiya ta duniya WHO, ta ayyana kasar Liberiya a matsayin kasar da ba ta da Ebola, amma daga bisani kuma cutar ta sake bulla a kasar.