Za a yi dokar masu suka ba hujja

Hakkin mallakar hoto Bala Naallah Facebook
Image caption Sanata Bala Na'allah ne ya gabatar da kudirin.

Majalisar Dattawan Nigeria ta fara wani yunkuri na samar da wata doka wadda za ta tanadi hukunci a kan duk wani ko wadansu da suka gabatar da koke a zauren Majalisar ko hukumomin gwamnati, ko kuma suka yi amfani da kafofin sadarwa na Internet wajen sukar wasu jami'an gwamnati da aikata laifuffuka ba tare da kwararan hujjoji ba.

Wannan yunkuri na 'yan Majalisar Dattawan dai ya janyo ka ce-na ce a kasar, inda wasu ke zargin 'yan Majalisar da yunkurin tauye 'yancin fadin albarkacin baki ga 'yan kasar.

Sanata Bala Ibn Na'allah, shi ne ya gabatar da kudirin ya kuma shaida wa BBC cewa ya yi hakan ne don ganin an samu tsari a yadda ake yin wasu abubuwa a kasar.

Ya ce "Bai yiwuwa a bar mutane sakaka suna zama cikin zaurensu suna rubuta korafi kan jama'a, ya kamata a dinga hakan bisa tsari."

Sanata Na'allah ya kara da cewa mutane suna da damar fadin albarkacin bakinsu idan har dokar ba ta yi musu ba.