"Mutane 600m na yin rashin lafiya saboda cin gurbataccen abinci"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabar Hukumar lafiya ta duniya WHO, Margaret Chan

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce a kalla mutane miliyan 600 ne suke yin rashin lafiya sakamakon cin gurbataccen abinci kowacce shekara.

A kiyasinta na farko da ta yi na duniya baki daya kan illar cin gurbataccen abinci, WHO ta gano wasu abubuwa fiye da talatin da suke gurbata abinci kamar su kwayoyin bakteriya da virus da toxins.

Afrika da kudu maso gabashin Asiya su ne yankunan da wannan illa ta fi yawa, kuma yawanci ta fi shafar yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Kusan kashi 40 cikin 100 na mutanen da ke yin rashin lafiya sakamakon cin gurbataccen abinci a duniya 'yan Afrika ne.