An kammala yakin neman zabe a Bayelsa

Gwamnan jihar Bayelsa Serikae Dickoson Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamnan jihar Bayelsa Serikae Dickoson

A ranar Asabar ne za a gudanar da zaben gwamna a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, inda 'yan takara ashirin daga jam'iyyu daban-daban za su fafata.

Tshohn shugaban kasar Goodluck Jonathan dan asalin jihar ne.

Wakilin BBC ya ce har ya zuwa daren Alhamis 'yan takarar suna ta kokarin nade tabarmar yakin neman zabe, abin da wannan karon ake ganin ya zo da bambanci.

Hukumar zabe ta ce ta kammala shirye shiryen gudanar da zaben.

A nata bangaren, rundunar 'yan sanda ta jihar Bayelsa ta ce ta tsauraran matakan tsaro gabanin zaben.