Amurka na tuhumar jami'an FIFA su 16 da rsahwa

Loretta Lynch babbar mai gabatar da kara  na Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Loretta Lynch babbar mai gabatar da kara na Amurka

Masu gabatar da kara a Amurka sun sanar da sabbin zarge zarge akan wasu jami'an kwallon kafa su goma sha shida, wadanda keda alaka da wani binciken badakalar cin hanci da rashawa a hukumar kwalllon kafa ta FIFA

Wadanda ake zargi sun hada da mambobi masu ci, ko kuma tsoffi, na kwamitin zartarwa na FIFA, da kuma tsohon shugaban Honduras Rafael Callejas.

Babbar mai gabatar da kara a Amurka ta ce a cikin fiye da shekaru ashirin, wadannan mutane sun hada kai wajen karbar dala miliyan dari biyu a matsayin cin hanci

A nata bangare hukumar FIFA tace zata cigaba da yin aiki tare da hukumomin Amurka, sannan ta sanar da sabbin sauye sauye