An kona ofishin INEC na Kogi

Image caption Nick Dazang ya ce karamar hukumar Dekina ta yi kaurin-suna wajen tayar da rikici.

Wasu mutane sun kona ofishin hukumar zaben Najeriya, INEC da ke jihar Kogi, kwana guda kafin a kammala zaben gwamnan jihar.

Kakakin hukumar zaben na kasa, Mista Nick Dazang, ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba a san mutanen da suka kona ofishin da ke karamar hukumar Dekina ranar Juma'a ba.

A cewarsa, "Da ma karamar hukumar Dekina ta yi kaurin-suna wajen tayar-da-zauen-tsaye. An taba kwace kayayyakin zabenmu a garin, shi ya sa ma ba mu kai kayan zaben [Asabar] wajen ba".

Mista Nick ya ce kona ofishin ba zai shafi zaben da za a yi ba saboda babu kayayyakin zabe a cikin ofishin lokacin da aka kona shi.

A ranar Asabar ne za a kammala zaben jihar, wanda aka ayyana a matsayin "wanda bai kammala ba" jim kadan kafin mutuwar dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Abubakar Audu.