An yi tuntuben alkalami wajen rubuta tarar da aka ci MTN

Hakkin mallakar hoto
Image caption An ragewa MTN tarar da aka sanya masa

Hukumar kula da harkar sadarwa a Najeriya, NCC, ta ce an yi kuskure wajen bayyana ragin da aka yi a kan tarar da kamfanin sadarwa na MTN zai biya.

Ranar Alhamis kamfanin na MTN mai hedkwata a Afirka ta Kudu ya ba da sanarwa cewa an rage kudin tarar zuwa dala biliyan uku da digo hudu a maimakon dala biliyan biyar da digo biyu da aka bukaci ya biya tun da farko.

Sai dai hukumar ta NCC ta ce tuntuben keken rubutu aka samu amma ragin da aka yi na kashi 25 ne cikin 100 na salain tarar.

Jiya Juma'a ne dai kamfanin na MTN ya ce an yi masa karin dala miliyan 500 a kan ragin da aka yi tun farko, lamarin da ya sa tara a yanzu za ta tashi a kan dala biliyan uku da miliyan 900.

Sai dai kakakin hukumar ta NCC, Tony Ojobo, wanda ya yi karin haske game da lamarin, ya bayyana cewa kuskure aka samu a wajen rubutu, don haka ragin ba dala biliyan uku da miliyan 400 ba ne kamar yadda MTN ya fada da farko.

A cewar Mista Ojobo, ragin da aka yi na kashi 25 cikin dari ne na asalin kudin tarar, ke nan abin da kamfanin zai biya yanzu ya tashi dala biliyan uku da miliyan dari tara.

Kamfanin na MTN ya ce yana kyakkyawan nazari a kan wasikun da hukumar ta NCC ta aike masa, kuma shugaban kamfanin zai sake tattaunawa da hukumomin Najeriya.

Ranar 31 ga watan Disamba ne dai wa'adin da aka debarwa kamfanin don ya biya sabuwar tarar zai cika.

Masu amfani da layukan waya na kamfanin MTN a Najeriya sun haura miliyan 62.

A watan Oktoba ne dai hukumar ta NCC ta kakabawa kamfanin tara saboda ya kasa yin rajistar layuka miliyan biyar da dubu dari.