An takaita zirga -zirgar ababen hawa a Bayelsa

Birnin Yenagoa
Image caption Birnin Yenagoa

Rahotanni daga jihar Bayelsa sun ce an takaita zirga zirgar ababen hawa a Yenagoa babban birnin jihar ta Bayelsa inda za a gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar Asabar.

Wakilin BBC da ke ce can Yenagoa ya ce da tun da karfe 6 na safe ma'aikatan zabe suka halara ofishin hukumar zabe domin karban kayayakin zabe.

'Yan takara daga jam'iyuu daban daban ne za su fatatata da juna a zaben gwamnan jihar Bayelsa.