Ambaliya ta shafi daruruwan mutane a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ambaliyar ruwa a arewacin Ingila

Ambaliyar sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi, ta tilasta wa daruruwan mutane a arewacin Ingla da kuma kudancin Scotland barin gidajensu.

Fiye da karo 50 a na gargadin yiwuwar fuskantar babbar ambaliyar ruwa, abin da ke nufin za a iya rasa rayuka.

Hukumar kwana-kwana a Cumbria, dake arewa maso gabashin Ingla ta bayyana ambaliyar a matsayin wacce ba a taba ganin irin taba.

Ambaliyar ta ratsa ta kauyuka da garuruwa, yayin da rafuka suka rika cika suna batsewa.

Wasu mutanen sun yi cirko-cirko a cikin motocinsu, wasu sun makale a wuraren aiki, yayin da ruwa ke kama wa mutane kunguru.