An kashe mutane 27 a hare-hare a Chadi

Hakkin mallakar hoto Reuters

A kalla mutane 27 aka kashe wasu fiye da 80 kuma sun jikata a wasu hare haren bama bamai ukku a Chadi.

Majiyoyin tsaro a N'Djamena babban birnin kasar sun ce an aka kai harin ne a wani yankin tsibiri a kasar ta Chadi.

Yan kunar bakin waken ukku sun tarwatsa kan su ne a wurare daban daban guda ukku a wata kasuwar da ke ci mako mako dake tsibirin Loulou Fou.

Wani mutum wanda ya bukaci a saya sunansa saboda dalilai na tsaro ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP aukuwar harin a yankin wanda hukumomi suka sanyawa dokar ta baci a watan da ya gabata saboda karuwar hare haren Boko Haram.