Matsaya kan daftarin sauyin yanayi

Hakkin mallakar hoto PA

Mahalarta taron koli kan sauyin yanayi a Paris sun gabatar da wani jadawali domin amincewa kan yadda za a rage dumamar duniya. Daftarin har ila yau ya kunshi wasu shawarwari masu sarkakiya. Wakiliyar Faransa kan batun sauyin Laurence Tubiana ta ce daftarin ya baiyana kudirin mahalartar na cimma yarjejeniya ko da yake akwai manyan batutuwan siyasa wadanda har yanzu ba'a warware su ba. A mako mai zuwa ministoci za su tattauna a kan daftarin inda ake fatan cimma masalaha bayan tsawon shekaru hudu ana muhawara a kan batun. Wakilai daga kasashe 195 ke halartar taron sauyin yanayin a Le Bourget dake kusa da Paris.