Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zaben Bayelsa an sami yamusti a kudancin Ijaw

Image caption Masu zabe a jihar Bayelsa

A Najeriya yayin da a yau ake gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa rahotanni na cewa an sami hargitsi a karamar hukumar kudancin Ijaw a jihar Bayelsa inda wasu yan bindiga suka tada fitina da kuma harbe harbe lamarin da ya jawo tsaiko wajen gudanar da zabe a karamar hukumar. Sai dai kuma zaben na gudana lami lafiya a sauran kananan hukumomi bakwai na jihar ta Bayelsa. Mr Nick Dazang mataimakin Daraktan yada labarai na hukumar zaben ya yiwa Aisha Sharif Bappa karin bayani game da halin da ake ciki.