An tuhumi Firaministan Malaysia da cin hanci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firaministan Malaysia Najib Razak ya musanta zargin cin hanci

Mahukunta a Malaysia sun yiwa Firaministan kasar Najib Razak tambayoyi a wani bangare na bincike game da zargin cin hanci da ake masa.

A cikin wata sanarwa, Hukumar yaki da ayyukan cin hanci da rashawa ta kasar ta ce an shafe sa'oi biyu da rabi ana yi masa tambayoyi.

Tunda farko an wallafa batun zargin aikata cin hancin ne a cikin wata mujalla mai suna Wall Street a watan Yuli.

Mujallar ta rawaito cewa an tura fiye da dala miliyan dari shida cikin asusun ajiyar banki na Firaministan.

Sai dai kuma ana ta sukar jan kafar da mahukuntar kasar ke yi wajen bayar da cikakken bayani a kan zargin da ake masa.

Tuni dai Mr Najib ya musanta zargin da ake yi masa.