Sojoji sun kama wani madugun kungiyar Boko Haram.

Rudunar sojin kasa ta Najeriya ta sanar cewa sojojinta sun kama wani da ake zargin shi ne shugaban masu daukar hoto na kungiyar Boko Haram wanda kuma ya ke cikin jerin sunayyen ' yan kungiyar da ake nema ruwa a jallo.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriya ya sanyawa hannu kanar Sani Usman Kuka Sheka , ta ce sojoji sun capke Abdullahi Abubakar Sadik ne a garin Uba da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.

Ta kuma ce sojojin sun kama wasu mutane hudu da ake zargin mambobin 'yan kungiyar ta Boko Haram ne a garin Rumirgo da kuma Kilakasa