'Yan IS sun kai hari birnin Aden

Shugaban Yemen Abdrabbuh Mansour Hadi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawaye ma kabilar Houthi sun mamaye wasu garuruwan kasar.

Wani bam ya tashi a birnin Aden da ke kudancin kasar Yemen, inda ya hallaka gwamnan birnin.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin da ya hallaka masu tsaron lafiyar Gwamnan da dama.

Gwamna Ja'afar Mohammed Sa'ad na sahun gaba-gaba a masu marawa dakarun gwamnatin Yemen baya wadanda suka fatattaki 'yan tawaye na kabilar Houthi daga babban birnin kasar Sanaa a farkon wannan shekarar.

Ya yin da shugaban kasar Abdrabbuh Mansour Hadi ya ayyana Aden a matsayin babban birnin kasar na wucin gadi a watan Yulin da ya wuce.

'Yan tawayen Houthi na zaune ne a arewacin kasar, kuma sun karbe iko da yawancin sassan Yemen ciki kuwa har da birnin Sanaa.