Ana zaben kananan hukumomi a Faransa

Masu kada kuri'a a kasar Faransa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana gudanar da zaben cikin tsauraran matakai.

An fara kada kuri'a a zaben kananan hukumomi a kasar Faransa, makwanni uku da kai mummunan hari birnin Paris wanda magoya bayan kungiyar IS mai ikirarin kafa daular musulunci suka kai.

An dai kada kuri'ar cikin tsauraran matakan tsaro, ya yin da tuni aka ayyana dokar ta baci a cikin kasar ba ki daya.

Wasu dai na ganin cewa jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta National Front wadda ke kokarin alakanta matsalar Ta'addanci da kwararowar 'yan cirani ta na samun farin jini tun bayan kai wannan hari.