Ghana ta kori alkalai 20

Image caption Alkalin Alkalai ta Ghana Geogina Theodore Wood

Gwamnatin Ghana ta kori alkalai 20 wadanda aka samu a badakalar cin hanci da rashawa .

Alkalan na kananan kotunan shari'a an zarge su ne da karbar cin hanci domin sauya hukuncin shari'a.

A baya Gwamnatin Ghana ta dakatar da bakwai daga cikin alkalan babbar Kotun kasar su 12 da ake zargi da laifin karbar cin hanci domin juya shari'a, ta kuma wanke daya

Wani dan-jarida mai bincike Anas Aremeyaw ne dai ya dauki hotunan bidiyon alkalan a lokacin da ake zargin suna karbar hancin.

Dan jaridan ya ce yana da faifan bidiyo na kusan sa'oi 500 a matsayin hujja na abin da alkalan suka aikata, wanda aka gabatar wa Alkalin Alkalan kasar.

Tun daga wancan lokacin aka kafa kwamitin bincike.

Kwamitin binciken ya ci gaba da binciken sauran alkalan da ake zargi.