Amurka ta kashe sojojin Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta ce ba ta kai hari kan sansanin sojin Syria ba.

Jiragen saman gamayyar kasashen da Amurka ke jagoranta sun kashe sojojin Syria akalla uku a wani hari da suka kai gabashin kasar.

Gwamnatin Syria ta yi Alla-wadai da harin, wanda aka kai a lardin Deir al Zor, tana mai bayyana shi da cewa "kutse ne na kai-tsaye" a cikin kasarta.

Sai dai gamayyar sojin ta musanta cewa jiragenta sun kai hari kan sansanonin sojin Syria, wurin da ba shi da nisa da yankin da ke hannun 'yan kungiyar IS.

Idan har wannan hari ya tabbata, to wannan shi ne zai kasance karon farko da gamayyar ke kai hari irin wannan tun da ta kaddamar da hare-hare a Syria a shekarar da ta gabata.