Trump na so a hana Musulmai shiga Amurka

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mista Donald Trump

Mutumin da ke son yin takarar shugaban Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya yi kira a hana Musulmai shiga kasar kwata-kwata.

Mista Trump ya ce wani sakamakon jin ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa Musulmai da yawa ba sa son Amurka, kuma ya kamata a kare mutanen kasar daga wannan barazana har sai an gano dalilin da ya sa Musulmai suka tsani kasar.

Dan takarar ya kuma ce ya kamata gwamnatin Amurka ta rika sa ido a Masallatai domin sanin me ake gudanarwa a cikinsu.

Kalaman Mista Trump sun zo ne bayan wasu kwanaki da wani mutun da matarsa suka kashe mutane 14 a California.

Hukumar tsaro ta FBI ta ce mutanen da suka bude wutar, sun dauki tsatssaurar akidar Islama.

Trump yana shan suka

Sai dai kalaman na Mista Trump sun janyo masa suka daga bangarori daban-daban, ciki har da fadar shugaban kasar ta White House.

Mataimakin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Mista Ben Rhodes ya ce kalaman na Mista Trump sun sabawa kyawawan akidun Amurka.

Shi kuwa Jeb Bush, abokin takarar Mista Trump, a jam'iyyar Republican ya ce Mista Trump "Ba shi da kan gado".

Ita ma wacce take kan gaba a zama 'yar takarar shugabancin Amurkan a jam'iyyar dimokrat Hillary Clinton a shafin ta na Twitter ta ce kalamin na Trump abin Allah wadai ne, wanda zai raba kawunan Amurkawa.

Da ma lokacin da yake yakin neman zabensa, Mista Trump ya jefa jam'iyyarsa ta Republican cikin rudanin kin jinin shigar baki kasar.

Yanzu da ya yi kiran a hana dukkan Musulmai shiga Amurka, ko da kuwa don yawon bude ido ne, ya kara jefa kansa cikin tsaka mai wuya, da ko dai sauran abokan hamayyarsa a jam'iyyar su mara masa baya, ko kuma ya ji shi kadai da kiran ruwan da ya yi.