'Ba mu ga 'yan matan Chibok ba'

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babu yammatan Chibok a cikin wadanda aka kubutar

Mahukunta a Kamaru sun ce 'yan matan makarantar Chibok da 'yan boko haram suka sace a bara ba sa cikin mutane 900 da rundunar sojojin yankin tafkin Chadi ta kubutar.

A makon da ya gabata ne wasu da aka kubutar suka ce akwai yiwuwar 'yan matan na daga cikin wadanda aka kubutar.

Kazalika sojojin sun ce sun kashe akalla mayakan boko haram 100 a wani samame bayan jerin hare-haren da suka kai.

An kwashe wadanda aka kubutar din a cikin motoci inda aka kai su garin Maroua, ana kuma ba su abinci da ruwa da kuma sauran kayan amfanin da suke bukata.

A watan Afrilun bara ne aka sace yan matan su kusan 200 a lokacin da suke cikin makaranta.

Sace yan matan ya ja hankalin kasashen duniya inda kowa ya yi Allah wadai da hakan.