China: An rufe wurare don kyautata muhalli

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yanayi a birnin Beijing ya zama tamkar dare ne

An rufe makarantu da masana'antu da kuma wuraren gine-gine a birnin Beijing na China a matsayin wani yunkuri na rage yawan iska mai gurbata muhalli a birnin.

Kazalika, an hana rabin motocin da ke hawa kan titunan kasar fitowa.

Ana sa ran za a ci gaba da daukar wannan mataki har zuwa ranar Alhamis.

Ana dora alhakin faruwar hayaki mai gurbata muhallin ne, kan wasu masana'atun da ake kera gawayi, da damshin iska da kuma yanayin hunturu.

Ba dai a iya hangen abin da ya wuce mita dari a birnin na Beijing.