Wutar daji ta yi barna a Damagaran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wutar daji ta yi barna a sama da eka 52,000 a Jamhuriyar Nijar

Wutar daji ta yi sanadiyyar hasarar eka 52,000 a Damagaram jamhuriyar Nijar.

A hirarsu da BBC babban darakta kula da gandun daji na jihar ya ce a wata biyu an samu tashin gobara dajin har sau18.

A cewar babban daraktan, jimillar fadin filin da wutar ta yi barna zai kai eka 52,000.

Cikin yankunan da wutar ta yi barna a cewarsa, sun hada da Goye da Tanout da Barbaje da kuma Damagaram ta kudu.

Babban daraktan ya ce hukumarsa na iya bakin kokarinta na wayar da kan jama'a kan amfani da wuta musamman a wannan lokaci na hunturu.