Ana tozartawa masu adawa a DRC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Jahuriyar Dimokradiyyar Congo, lokacin da ya ke jawabi a wani taron da ya hada da masu adawa da gwamnatinsa.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama a kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo watau DRC, sun yi gargadin cewa wadanda ke adawa da gwamnatin kasar, na fuskantar tozartawa, har wasu lokutan ma an kashe su gabannin yakin neman zaben da za a yi a badi.

Rahotanni sun ce an yi kashe-kashen da ke da alaka da wannan zabe a kalla sau 20.

Rahotanni sun ce an tsare sama da mutane 600, wadanda yawanci suke adawa da duk wani yunkurin da Shugaban kasar Joseph Kabila ya ke yi domin rike mulki kafin wa'adin mulkinsa ya shude karshen wannan shekarar.

Ministan shari'a na kasar dai ya soki rahoton, inda ya ce bai yi adalci ba, kuma akwai zarge-zarge da dama da basu da makama a ciki.