An bayar da belin Oscar Pistorius

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Oscar Pistorius na fuskantar yiwuwar sake shan dauri.

Wata kotun Afrika ta kudu ta bayar da belin dan tseren nan na kasar, Oscar Pistorius, kafin a yanke masa hukunci bayan an same shi da laifin kisan budurwarsa, Reeva Steenkamp da gangan.

Kotun za ta yanke masa hukunci ne a ranar 18 ga watan Aprilun shekarar 2016.

Kazalika, kotun ta bukaci dan tseren ya biya £450 kafin ta bayar da belinsa.

Haka kuma za a ci gaba da yi wa Mista Pistorius daurin talala sannan za a sanya masa na'urar da za ta rika gane duk inda ya je, sai dai zai iya fita daga gidansa a kullum daga karfe bakwai na safe zuwa tsakar rana domin yin tafiyar da ba ta wuce kilomita 20 ba.

Kotun ta kuma bukaci Mista Pistorius ya mika mata fasfo dinsa.

Yana fuskantar daurin shekara 15 - ko da ya ke alkalin kotun na da damar yi masa sassauci.

Mista Pistorius ya amince cewa ya harbe budurwarsa a shekarar 2013, sai dai ya ce ya yi zaton dan fashi ne ya shiga gidansa.