Za a yi kuri'ar raba gardama a Rwanda

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan hamayya sun ce Kagame ba ya son a rika sukarsa.

Hukumomi a Rwanda sun ce za a yi kuri'ar raba gardama domin bai wa Shugaba Paul Kagame damar yin ta-zarce a karo na uku.

Hukumomin sun ce za a kada kuri'ar ne ranar 18 ga watan nan.

A watan jiya ne dai 'yan majalisar dokokin kasar suka amince su sauya kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa Mista Kagame damar sake yin takara bayan mutane miliyan uku sun yarda da hakan.

An dora alhakin sake gyara kasar ta Rwanda kan Shugaba Kagame bayan kisan kare-dangin da aka yi a shekarar 1994, sai dai 'yan hamayya sun ce ba ya jure irin sukar da ake yi wa gwamnatinsa.